ABNA24 : Masharhancin wanda tashar talabijin din CNN ta yi hira da shi ya kara da cewa hakan abu ne mai yiyuwa saboda yadda shugaba mai ci a yanzun Donald Trump ya ki yin alkawalin mika mulki cikin ruwan sanyi idan ya sha kaye a zabe.
Al’ummar kasar ta Amurka suna fargabar cewa idan har shugaban kasar Donald Trump ya ki mika mulki ga John Beidan inda aka kayar da shi a zaben da za a yi a ranar 3 ga watan Nuwamba na wannan shekarar, kasar za ta fada cikin rikicin siyasa mai hatsari da zai kai ga fada da makami.
Fredman ya kara da cewa; Na fara aikina na jarida ne da fara daukar labarin yakin basasar Lebanon, yanzu kuma ina jin tsoron cewa zan kare aikina na jarida da daukar labarin yakin basasar Amurka na biyu wanda mai yiyuwa ne ya faru.
342/